Akalla mutum daya ya rasa ransa, an kuma yi awon gaba da dalibai da malamai a Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zaria a jihar Kaduna a arewacin Najeriya, bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari makarantar.
Wata majiya daga kwalejin wacce ta nemi a sakaya sunanta saboda ba a ba su umarnin su yi magana kan lamarin ba, ta tabbatar da aukuwar lamarin.
“Tun da misalin karfe 10 na dare suka shiga makarantar, ba su fita ba har sai karfe dayan dare.” In ji majiyar.
‘Yan bindigar sun far wa makarantar ne a daren Alhamis, wannan kuma shi ne karo na uku da ake kai hari a kwalejin.
Bincike ya nuna cewa mutum takwas aka sace, kana an kashe dalibi daya an kuma jikkata wani guda. Kokarin jin ta bakin hukumomin jihar ya ci tura.
Jaridar Daily Trust ta ce, malaman da aka sace sun hada da Mr. Habila Nasai da Mr. Adamu Shehu.
Wannan hari na zuwa ne kasa da mako biyu bayan sako daliban jami’ar Greenfield da aka sace tun a watan Afrilu a jihar ta Kaduna, wacce kef ama da hare-haren ‘yan bindiga.