Yin rijistar, zai ba mazauna yankin damar samun wani katin shaida a wani mataki na tabbatar da tsaro.
Cibiyar wadda aka samar da kayayyakin sadarwa na zamani a cikin ta, za ta rinka tattarawa, da adana bayanai da kuma bada katin shaida ga duk dan asalin yankin na Ungogo.
Abdullahi Garba Ramat dake zaman shugaban karamar hukumar ta Ungogo ya ce batun tsaro na daga dalilan samar da wannan cibiya.
Ko da yake, galibin mazauna yankin na Ungogo na da karancin masaniya game da wannan sabon tsari, amma ga alama sun yi maraba da shi.
Tuni dai hukumar NITDA mai bunkasa harkokin fasahar sadarwa a Najeriya ta bayyana aniyar tallafawa wannan tsari, in ji Shiekh Lawan Abubakar da ke zaman mai tsare-tsarea shiyyar arewa maso yammacin Najeriya na hukumar.
Karamar hukumar Ungogo dai na cikin kananan hukumomi 8 na kwaryar birni da kewayen Kano kuma wasu sassa na manyan hukumomin gwamnatin tarayya, kamar filin jirgin sama na Kano da Jami’ar Bayero na cikin yankunanta.
Saurari cikakken rahoton a ciki sauti: