Kaduna: Al’umar Birnin Gwari Ta Kuduri Aniyar Yaki Da Mahara

Gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai

Al’umar masarautar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna ta kuduri anniyar tashi tsaye ta nemi gafara wurin Ubangiji kana ta yaki bata garin da ke yawan kai masu hare hare suna mamaye wasu garuruwansu tare da kwace masu gonaki da gidaje

Yawan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai masu ya sa al’umar Birnin Gwari dake cikin jihar Kaduna kira taron addu’o’i tare da ayyana anniyar hada kai domin su yaki muggan mutanen.

Yayinda yake jawabi a wurin taron mai martaba sarkin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Jibrin wanda yake murnar cika shekaru 26 akan mulki ya jawo hankalin al’ummar akan bukatar dake akwai domin tabbatar sun dakile duk wata tashin tashinar dake damunsu.

Ya yi kira ga jama’arsa su nemi gafara wurin Ubangiji domin Allah kadai ne zai iya maganin fitinar. Ya tuna da lokacin da ya fara mulki yadda ‘yan bindiga suka taso masu. Lokacin sun kwace wasu wurare a masarautar amma an koresu. Sai dai duk da korar da ake yi masu suna komawa su sake mamaye wasu wurare.

A cewar sarkin zasu iya maganin ‘yan bindigan. Yace ya taba rubutawa gwamnati akan hakan. Yana son gwamnati ta sani cewa akwai maza gaggararru cikinsu da a shirye suke su sadakar da kansu domin su kare kasar su.

Shi ma Dan Masanin Birnn Gwari Alhaji Zubairu Abdu wanda ya gabatar da wata kasida y ace maganar tsaro a masarautarsu magana ce mai tsawo saboda a shekarar 1993 zuwa 1995 an yi wani atisayi inda mazan masarautar suka fita suka yi azama, suka shiga dazuka suka yi maganin bata gari. Ya gayawa Sarki Zubairu matasan karamar hukumar ashirye suke a yi gudunbala, su yi maganin wadanda suka hanasu zaman lafiya.

Wadanda suka taba fadawa hannun bata garin sun bayyana irni azabar da suka sha. Wani ya ce sun yi masu fashi suka amshe ‘yan kudin dake hannunsu kana suka shiga dasu daji inda suka sasu kwantawa bayan sun yi tafiyar wajen kilomita biyar. Akwai wanda ya ce sun tilasta masu barin garin da aka haifesu inda suke da gonaki da gidaje. Sun raba su da iyalansu domin basa wuri daya.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

KADUNA: Al’ummar Birnin Gwari Zasu Yaki Masu Kai Masu Hari - 4’ 20”