Kada Ku Yadda Da Sabon Kudin ECO Na Faransa - Boube Namaiwa

Farfesa Boube Namaiwa

Kasashen Afrika ta yamma goma 15 sun amince su fara amfani da kudin bai daya a shekara ta 2020 da ake kira Eco.

Kawunan masana ya rabu akan irin tasiri da kudin zai yiwa tattalin arzikin yankin, musamman mambobin kasashe 8 masu yin amfani da Cfa franc, wanda kasar Faransa take goyon baya.

Kungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta yamma (wato ECOWAS), da kungiyar tattalin arziki da kuma siyasar yankin, sun ce za a fara aiki da kudin a hankali tare da kasashen da suka cika dukkan sharuddan da ya kamata na shiga tsarin da farko.

A cikin hirar sa da Sashen Hausa na Muryar Amurka, Farfesa Boube Na Mewa, mai fashin baki akan siyasar duniya na jami’ar Diop a kasar Senegal, ya ce kasar Faransa ta kewaya duka kasashen 8 daga cikin 15 na kungiyar ECOWAS, wadanda ta yiwa mulkin mallaka ta bayyana musu cewa ita ma za ta shiga cikin sabon kudin Eco.

Na Mewa ya ce har yanzu kasar Farasa bata janye daga cikin kasashen da ta yiwa mulkin mallaka ba, saboda wadan nan kasashen 8 su za su sako Faransa a ciki, don haka ya shawarci Najeriya da tafi ko wace kasa karfin tattalin arziki kar ta bari Faransa ta shiga cikin tsarin kudin Eco.

“Abin da ‘ECOWAS’ take dauke da shi shine cewa zamu buga kudin mu anan gida kuma zamu karfafa shi idan mun ga kayanmu suna shiga a cikin duniya, kuma ya kamata a saka sauran kasashen da basa amfani da kudin CFA guda 7 da kuma sauran 8 da suka zama 15” a cewar Farfesa Boube Na Mewa.

Farfesa Na Mewa ya ce yanzu haka Faransa ta fara wata dabara, inda shugaban kasar Emmanuel Macron ya kai wata ziyar ga shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara, da suka fito da wani kudin Eco na kasashe 8 masu yin amfani da CFA.

Wanda suka ce sun kawo sauyi a cikin sabon kudin da za su yi na Eco, inda suke fatan Najeriya da Ghana da kuma sauran kasashen za su amince nan gaba a shigo da Faransa ciki.

Ya ce wannan Eco da aka yi sun ci amanar wancan Eco na ‘ECOWAS’ da aka yi har sunan ma kuma sun yi satarsa ne.

Farfesa Na Mewa ya ce ribar da wannan kudi na Eco ga kasashen Afirka ta yamma shine zai taimaka musu su karfafa kudinsu ko su rage masa daraja don kayayyakinsu su samu su shiga cikin kasuwannin duniya.

Sannan kuma kasashen su za su buga kudaden nasu bawai wata kasa ta buga musu ba, kana hada-hadar kasuwanci a tsakanin kasashen goma 15 za ta yi sauki, inda zaka iya daukan kaya ka sayar a tsakanin kasashen ba tare da neman canji kudin waje ba da hakan zai sanya su rage yin amfani da dala da CFA da dai sauransu.

Saurari cikakkiyar hirar da Alheri Grace Abdu ta yi da Farfesa Boube Na Mewa:

Your browser doesn’t support HTML5

Kada Ku Yadda Da Sabon Kudin Eco Na Faransa - Boube Na Mewa