A lokacin da yake yiwa manema labarai karin bayani, Shugaba Emmanuel Macron, ya ce yazo ne domin yiwa kasar Nijar gaisuwar ta’aziyya sabili da sojojinta da suka mutu a harin ta’adanci a barikin Inates da ke kan iyakar Nijar da Mali.
Shugaba Macron ya bayyana jimamin mutuwar sojojin, da kuma damuwa sabili da matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar ya kuma jadada goyon bayan Janhuriyar Nijar da kuma ci gaba da taimakawa a yunkurin shawo kan matsalolin tsaron da suke kara zama barazana ga yankin da kuma sauran kasashen duniya.
Shugaba Macron ya tabo irin sukar da kasarsa ta ke sha daga talakawan yankin Sahel, inda ya bukaci shugaba Issouhou da jam’iyyarsa mai mulki da su fito fili su bayyanawa jama’a cewa su suka bukaci Faransa ta girke sojojinta a kasar. Kana ya bukaci sauran shugabannin kasashen yankin Sahel da su fito suma su bayyana hakan.
A wani mataki na neman hada hannu, da kara fahimtar juna, Shugaban Faransa ya kirawo wani taro da sauran takwarorinsa na kasashen Mali, Chadi, Nijar, Burkina Faso, Mauritania da kuma Nijar, a ranar 13 ga watan Janairu mai zuwa.
A nashi jawabin, Shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ya bayyana godiya ga kasar Faransa saboda irin gudummuwar da take baiwa kasashen yankin Sahel a yakin da suke gwabzawa da ‘yan ta’adda da ya ja hankali kasashen yamma.
Kasar Faransa ta yi bakin jini a yankin Sahel sabili da ana gani kamar bata taka wata rawar gani a yunkurin yaki da ta'addanci da kuma shawo kan matsalar tsaro da ta addabi yankun duk da girke dakarunta da ta yi a yankin da sunan yaki da ta’addanci.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:
Facebook Forum