Shettima Ummar Abba Gana, shine mukaddashin shugaban hukumar raba kudaden shiga da tsara albashin jami’an gwamnatin Najeriya ya bayyana cewa duk jihar da aka shiga a kasar baza’a rasa samun albarkatun kasa ba, dan haka yakamata a bunkasa ayyukan hukumar raya albarkatun kasa domin budewa jama’a hanyoyin ayyukan yi da gwamnati kuma ta sami kudaden shiga, domin a cewar sa sauran albarkatun kasa sun bambanta da man fetur tun da shi a wuri guda kawai yake.
Amsa wannan kira yasa wani matashi Injiniya Baba Abba Dalori kafa cibiyar dogaro da kai ta hanyar Keke Napep a Abuja, wanda ya bayyana cewa bayan ya kammala ayyukan bautar kasa bai sami aikin gwamnati ba dan haka sai ya sayi Keke Napep guda wadanda yanzu haka suka rubanya har guda 170, kuma da wannan sana’a ya samawa matasa guraaben ayyuka kusan dari hudu.
Hajiya Sadiyya Mahmud, na daya daga cikin wadanda suk zuba jari a cibiyar kuma ta bayyana cewa duk da korafin da jama’ar kasa ke yi kan rashin kudi, ita kam sais am barka saboda tana ganin alat, wato kudin kabu kabun da ake yi mata kullum na shiga asusun ajiyar bankin ta.
Abdulkarim Hussaini daya daga cikin direbobin ya bayyana cewa da wannan aiki na tukin Keke Napep yake daukar dawainiyar matan sa biyu da kuma sauran iyalinsa, dan haka ya yi kira ga matasa kada su raina sana’a domin raina kadan ke haddasa zaman banza wanda kan kai ga shaye shaye da lalacewar rayuwa.
Domin Karinbayani, ga rahoton Nasiru Adamu Elhikaya.
Your browser doesn’t support HTML5