Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari Ya Kai Ziyarar Kwana Daya Jihar Osun


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Kamar yadda muka sanar jiya, yau shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kai ziyarar kwana daya zuwa jihar Osun dake kudu maso yammacin kasar

Ta bakin wani hadimin gwamnan mai bashi shawara akan harkokin baki dake zaune a jihar, musamman 'yan arewa, shugaban ya kai ziyara jihar ce domin ya taya jihar murnar kirkirota shekaru 25 da suka shude.

Ana kyatata zato lokacin ziyarar shugaban zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar yayi, musamman wasu makarantu na mausamman da gwamnan ya gina da aka ce, wai babu irinsu a duk fadin Najeriya.

Gwamnan ya gina makarantu na makiyaya Fulani da kuma na boko tsantsa da suka hada da matakin firamare da na sakandare.

Baicin kaddamar da ayyukan, shugaban zai sadu da al'ummar jihar da manyan jami'an gwamnati tare da nuna godiyarsa saboda zabensa da suka yi.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG