Joshua Wong Ya Shiga Zanga Zangar Hong Kong

Wong ya yi hasashen cewa, muddin aka bar, Carrie Lam, ta ci gaba da zama a mukaminta, za’a kara samun mutane da dama da za su shiga wannan fafutukar har sai ranar da “muka samu muhimman hakkokinmu da kuma ‘yancinmu.”

Wani mai rajin kare dimokradiyya a Hong Kong, Joshua Wong, ya shiga sahun masu goyon bayan kiran da ake yi wa shugabar yankin na Hong Kong mai goyon bayan Beijing, da ta sauka daga mukaminta.

Wong ce da zaran ya fito daga gidan yari a yau Litinin, zai shiga gagarumar zanga zangar da ke adawa da dokar da ake so a samar, wacce za ta ba da damar a mika masu laifi ga China don a tuhume su.

Wong ya yi hasashen cewa, muddin aka bar, Carrie Lam, ta ci gaba da zama a mukaminta, za’a kara samun mutane da dama da za su shiga wannan fafutukar har sai ranar da “muka samu muhimman hakkokinmu da kuma ‘yancinmu.”

Jami’ai sun sake bude hanyoyi a yau Litinin a kusa da shedkwatar gwamnati bayan daruruwan dubban masu zanga zanga dauke da bakin kyalle suka yi tattaki a jiya Lahadi akan kudirin dokar da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Sai dai masu zanga zangar sun sa harkokin kasuwanci da ayyukan gwamnati sun tsaya cik, yayin da wadanda suka shirya zanga zangar suke ikrarin mutum miliyan biyu ne suka yi tattaki akan tituna.