Dubban mutane sun bazama akan titunan birnin Hong Kong sanye da bakaken kaya a yau Lahadi, inda suka yi ta kira ga shugabar yankin Carrie Lam da ta sauka da mukaminta.
Masu zanga zangar sun nuna fushinsu ne, kan yadda shugabar ta tafiyar da batun wani kuduri da ya bukaci a mika duk wanda aka samu da aikata wani babban laifi ga China, domin a mai shari’a.
Wasu daga cikin masu zangar zangar sun yi tattaki dauke da furanni a hannunsu, cikin yanayi na tsananin zafi, inda suka taka tun daga wani wuri da ake kira Victoria Park zuwa ofisoshin gwamnati da ke tsakiyar birnin na Hong Kong.
A jiya Asabar, Shugaba Carrie Lam, wacce ke samun goyon bayan China, ta dakatar da batun shirin kirkirar dokar, ba tare da ta yi watsi da shi baki daya ba.
Facebook Forum