Shirin mika mulki na cigaba ba tare da wata matsala ba. Yau shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan da shugaba mai jiran gado Janar Buhari zasu gana.
Jajiberen mika mulkin shugaban kasa mai barin gado zai nunawa sabon shugaban fadar gwamnati. Yace sun karbi bayanan gwamnatin amma za'a mikawa shugaban kasa mai jiran gado takaitacen bayani a rubuce. Barrister Solomon Dalung ya kyautata zaton za'a mika mulki ba tare da wata tangarda ba.
Dangane da cewa matasalar rashin wuta ka iya ragewa bikin mika mulki armashi Solomon Dalung yace suna san da hakan amma daga jiya an soma samun sauki. Yace abubuwan da suka faru wani shiri ne na yiwa bikin zagon kasa da nufin shafawa gwamnati mai shigowa kashin kaza..
A bangarensu na gwamnati mai zuwa yace sun daura damara kuma babu gudu babu ja da baya. Kowane hali suka samu kansu zasu yiwa kasar aiki. Zasu yi iyakar kokarinsu saboda su dawo da daraja da mutuncin kasar.
Game da bikin mika mulki Solomon Dalung yace ganin irin halin da 'yan kasa ke ciki bai kamata a yi wani gagarumin biki ba. To saidai shirin bikin baya hannunsu yana hannun gwamnati mai barin gado ne wadda tana iya ta yi birgimar hankaka.
Yace 'yan Najeriya sun basu amana saboda haka babu wani dalilin yin wani babban biki. Talaka na fama da yunwa sai kuma azo ana shaholiya da dukiyarsu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5