John Mahama - Laifin Tsagerun Niger Dllta Ne, Karancin Wutar Lantarki Ya Addabi Kasar Ghana

Ghana, kasar da tattalin arzikinta shine na biyu a girma a yammacin Afirka ta fada cikin duhu sakamakon rashin wutar lantarki, lamarin da shugaban kasar John Mahama yake azawa kan zagon kasa da tsageru suke yi a yankin Niger Delta na Nijeriya.

A baya, kasar Ghana itace kasar da tattalin arzikinta yake habaka sosai a yammacin Afirka, amma yanzu rashin wutar lantarki da yawan kudade da gwmnati kasar tayi fiye da ‘kima da faduwar farashin kayayyakin da take fitarwa, yasa ta karbi bashin Dala Biliyan ‘daya daga babban asususn bada lamani na duniya IMF.

A jawabinsa na makon da ya gabata, shugaban kasa John Dramani, ya zargi rashin wutar da ake samu a Ghana da cewa ta samo asaline daga katsewar samun Man da ake a Najeriya, wanda shine ake amfani wajen samar da wuta a Ghana.

Katsewar samar da Mai da Mahama yake magana ta fara ne a farkon wannan shekara, lokacin da tsagerun Niger Delta dake kiran kansu Avengers, suka fara fasa bututun Mai tare da lalata wasu kadarorin mai a yankin na Niger Delta.

Wannan matsala ta sa masana suna ganin Najeriya tana iya fuskanci komadar tattalin arziki. Kazalika sunnce duk da cewa tsagerun sun janyo matsala, dawuya a azalaifin karancin mai daga Najeriya a zaman dalilin da yasa Ghana take fuskantar karancin hasken lantarki.