John Kerry Ya Gana da Shugaba Muhammad Buhari

Shugaba Muhammad Buhari

Yau a fadar shugaban Najeriya Muhammad Buhari an yi tattaunawa mai tsawon gaske tsakanin sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da shugaban Najeriya Muhammad Buhari a fadarsa ta Aso Rock dake Abuja babban birnin Najeriya

Ganawar ta hada da manyan jami'an gwamnatin Najeriya da na Amurka wadanda suke tawagar John Kerry.

A wani hannun kuma John Kerry ya gana da wasu gwamnonin wasu jihohin arewa domin tsara hanyoyin da kasar Amurka zata taimaka wurin bunkasa rayuwar al'umma da kuma yaki da ta'addanci da talauci da rashin aikin yi.

A wurin ganawar da Shugaba Muhammad Buhari Mr. Kerry ya jinjinawa Najeriya kwarai akan matakan da take dauka da kuma irin nasarorin da take samu wurin yaki da cin hanci da rashawa inda ya alakanta cin hanci da rashawa da ayyukan ta'addanci da kasar ke fuskanta.

Kamar yadda ya bayyana cin hanci da rashawa suna cikin bangaren dake kawo rashin aikin yi da kuma kuntatawa al'umma wurin kasa yi masu aiki da makudan kudaden da kasar ke tarawa domin raya kasar da taimakon al'umma.

Shi ma shugaba Buhari ya kara jaddada tsare tsare da hanyoyin da gwamnatinsa ke dauka na girka madafun yaki da cin hanci da rashawa akan yadda ko bayan wa'adinsa na mulki Najeriya zata samu kyakyawar turbar yaki da cin hanci da rashawa ba tare da komawa gidan jiya ba inda ake wawurar dukiyar jama'a.

Akan yaki da ta'addanci Shugaba Buhari ya yabawa kasar Amurka da irin goyon bayan da taimakon da take ba Najeriya. Amurka na ba Najeriya gudummawar kayan aiki da bayanan asiri har ta samu gagarumar nasara kan 'yan ta'ada.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

John Kerry Ya Gana da Shugaba Muhammad Buhari - 3' 25"