Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Shirya Karbar Bakoncin Sakataren Harkokin Wajen Amurka


Shugaba Buhari da John Kerry
Shugaba Buhari da John Kerry

Fadar gwamnatin Najeriya ta kammala shirin karbar bakuncin babban sakataren hulda da kasashen waje na kasar Amurka John Kerry.

Kamar yadda sanarwa daga ofishin jakadancin Amurka dake Abuja, ta bayyana Mr. Kerry zai ziyarci shugaba Mohammadu Buhari, domin tattaunawa akan harkokin tsaro da irin matakan da ake ‘dauka domin warware matsalar, da kuma sha’anin tattalin arziki da yaki da cin hanci da karbar rashawa harma da batun kare hakkin bil Adama.

A birnin Sokoto kuma ana sa ran Mr. Kerry, zai bada jawabi na musamman akan muhimmancin jajircewar al’umma da matakan da ake dauke don karya lagon amfani da addini don aikata ta’addanci, da yanzu a Najeriya da sauran kasashen musulmi a duniya ke fuskanta.

Kakakin shugaban Najeriya, Mallam Garba Shehu, yace tun farko ma shugaban Amurka Barack Obama ne yakamata kawo wannna ziyara Najeriya, amma ya nuna cewa idan har bai sami dama to sakatare Kerry ne zai kawo ziyarar. A cewar Mallam Garba, gwamnatin Amurka na taimakawa Najeriya ta fannoni da yawa, musamman harkar yaki da ta’addanci da kuma rashawa da cin hanci. Amurka kuma itace ta fi kowacce kasa taimakawa Najeriya yanzu a Duniya.

Saurari cikakken rahotan Murtala Faruk daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:54 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG