Jirgin Ruwa Mai Dakon Kayan Yaki Da Amurka Ta Tura Don Taimaka Ma Isra'ila Ya Kusa Isa Can.

USS Gerald Ford

Shugaban Turkiyya ya bayyana cewa jirgin yakin ruwan zai haifar da mumunar barna a Filasdinu.

ANKARA, Oct 10 (Reuters)

A jiya Talata, shugaban Turkiyya Reccep Tayyip Erdogan ya soki matakin Amurka na tallafa wa Isra’ila da jirgin ruwan yaki da a halin yanzu ke kan hanyarsa ta isa kasar Isra’ila sannan yana mai cewa wannan mataki zai kai ga yi wa ‘yan Filasdinu kisar mummuke a Gaza.

Biyo bayan harin bazatan da ‘yan Kungiyar Filasdinu na Hamas suka kai Isra’ila a ranar Asabar, a ranar Lahadi ne Sakataren tsaron Amurka Lyod Austin ya ce, Amurka zata tallafa wa Isra’ila da jirgin yakin ta na ruwa mai rukunin makaman da su ka hada da USS R, Ford kusa da Isra’ila.

Kafar labarai ta Reuters ta ruwaito cewa, Amurka ta girke jiragen yakin ta na sama a yankin kasar Isra’ila a matsayin gargadi ga Filasdinu. “ a ranar 8 ga watan Octoba ne Austin ya bada umarnin a matsa da jirgin ruwan mai suna Gerald R. Ford kusa da Isra’ila.