Wani jirgin fasinja dauke da akalla mutum 98 ya fadi a wani wuri mai yawan jama’a, dakiku kafin ya sauka yau Juma’a da rana a Karachi, birni mafi girma a Pakistan, ya lalata gine gine da dama dake kan wata karamar hanya.
WASHINGTON DC —
Hayaki da kura mai yawa ne suka turnuke wurin sakamakon hadarin jirgin a cikin yanayi mai zafi da aka samu yau da rana, kana mazauna karamar hanyar sun taimakawa aikin ceto.
Jirage masu saukar ungulu na ma’aikatar jiragen Sojin Pakistan sun kimanta barnar hatsarin kana sun yi aikin ceto. An riga dai an tura ma’aikatan bincike da gano mutane domin aikin ceto, a cewar wani sakon Twitter da mai Magana da yawun ma’aikatar sojin kasar Manjo Janar Babar Iftikhar ya aike.
Jirgin da ya taso daga filin saukar jirage na kasa da kasa na Pakistan yana kan hanyarsa ne daga Lahore zuwa Karachi inda yayi hatsari a wani wuri da ake kira Model Colony.