Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Kasashen Duniya Su Kaiwa Nahiyar Afrika Dauki - Antonio Guterres


Antonio Guterres
Antonio Guterres

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a kaiwa kasashen Afirka dauki a wannan bangare mai muhimmanci na yaki da annobar coronavirus, yana mai cewa akwai bukatar kasashen duniya su dau wannan matakin karfafa tsarin lafiya da rarraba abinci tare da kiyaye matsalar fatara a nahiyar.

A jiya Laraba, Guterres ya yabawa kasashen Afirka da kungiyar kasashen Afirka ta A.U, akan yadda suka dauki matakan killace jama’a da rufe kan iyakoki, da kuma tabbatar da aiki tare a nahiyar domin dakile yaduwar kwayar cutar.

Sai dai ya ce annobar, tana barazana ga bunkasar nahiyar Afirka da ake ganin zai tsananta rashin daidaito, karin matsalar yunwa, rashin abinci mai gina jiki da raunin kamuwa da cututtuka.

Baya ga yin kira ga kasashen duniya su tallafawa nahiyar, Guterres ya kuma yi kira ga kasashen Afirka da su tabbatar da rigakafin cutar na bai daya ga dukkan kasashen nan gaba kuma akan farashi mai rahusa.

Cibiyar kula da yaduwar cututtuka ta Afirka tace, COVID-19 ta kashe sama da mutane 2,800. Kasashen da cutar tafi kamari a nahiyar sun hada da Afirka ta Kudu, Misra, Algeria, Morocco da Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG