Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kasashen G-7 na Duba Yiwuwar Gudanar da Taron ta Kamar Yadda Ta Saba


Shugabannin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G-7 na duba yiwuwar karbar shawarar shugaban Amurka, Donald Trump, na gudanar da taron ta kamar yadda aka saba kowa ya hallara watakila a wata mai zuwa, yayin da adadin wadanda suka kamu da coronavirus a duniya ya haura miliyan 5.

Trump ya bayyana ra’yinsa a ranar Laraba a wani sakon Twitter, inda ya wallafa cewa "Amurka tana sake dawowa da karfinta".

"Sauran membobin ma sun fara dawowa daidai", Trump ya fada, "kuma hakan wata babbar alama ce na komawar harkoki kamar yadda aka saba".

Kakakin gwamnatin Japan, Yoshihide Suga ya fada yau Alhamis cewa, har yanzu suna duba yiwuwar halartar Firai Minsta Shinzo Abe, kana kuma kasashen biyu suna da dangantaka mai karfi.

Firai Ministan Canada, Justine Trudeau, ya ce zancen gudanar da taro na mutum da mutum ko ta yanar gizo ya dogara ne akan nazarin matakan kariya da aka dauka da kuma shawarwarin da masana suka bayar.

Ofishin Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya ce a shirye ya ke ya halarci taron, idan har yanayin lafiyar da ake da shi ya ba da dama, yayin da shugabar Jamus Angela Merkel ta ce, za ta jira ta ga abin da zai faru.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG