Jirgin Sama Mai Amfani Da Hasken Rana

Jirgin sama mai amfani da hasken rana

A kokarin jirgin saman nan dake amfani da hasken rana kadai na zagaya duniya, a safiyar Alhamis ya sauka a birnin Seville na kasar Spain bayan da ya tashi daga birnin New York.

Jirgin mai dauke da kujerar zaman mutum ‘daya kacal ya tashi ne daga filin saukar jiragen sama na John F. Kennedy a safiyar Litinin din da ta gabata a tafiye tafiyensa karo na goma sha biyar a kokarinsa na zagaye duniya.

Bertrand Piccard, ‘dan asalin kasar Swiss shine ke tuka wannan jirgi a kokarin zagaye duniya, yana tafiyar kilimita 70 a Awa.

Shi dai wanan jirgi nada manya manyan fuka fukai masu girman mita 72, wanda girmansa ya wuce girman Boeing mai lamba 747, haka kuma nauyinsa baifi nauyin motar hawa ba.

Jirgin dai ya fara wannan tafiya ne tun shekara ta 2015, kuma daga birnin Seville jirgin zai nufi Abu Dhabi.

Your browser doesn’t support HTML5

Jirgin Sama Mai Amfani Da Hasken Rana 0'54"