Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wayoyin Zamani Da Makamantan Su, Kan Haddasa Fitina Ga Al'uma!


Wayoyi da Kimiyyar Zamani
Wayoyi da Kimiyyar Zamani

Da akwai bukatar lokutta da dama mutane suyi amfani da hankalin su, wajen warware wasu matsaloli, musamman ma idan suka hada da abubuwan kimiyyar zamani, kamar su wayar hannu, kwamfuta, laptop, da dai makamantan su.

Wasu ma’aurata Christina Lee da mijinta Michael Saba, ita ‘yar jarida shi kuma Inginiya ne, suna da gidan su, a kusan kullun idan dare yayi sai mutane su buga musu da cewar network ya nuna musu cewar wayar su da aka sace tana gidan su.

Mafi akasarin wayoyin zamani suna dauke da wata manhaja da zai iya bayyana ma mutun inda wayar shi take idan an sace. Da dama idan mutane sun je gidan sai suyi musu bayani kan cewar, suba barayi bane kuma basu siyan kayan sata, don haka basu da wata waya a gidan su.

Abu dai yakai matuka sai suka sanar ma kamfanonin waya da cewar ana zuwa gidan su da sunan neman waya, koda aka duba sai aka gano cewar wai idan gida na tsakanin karfen da ke dauke da karfen kamfanin waya, shike haddasa wannan, shi ya nuna cewar waya tana gidan dake tsakanin falwayar biyu.

A takaice dai mutanen sun bukaci da kamfanonin su gyara wannan matsalar don gujema wata matsala da hakan kan iya haifarwa. Sai ai hattara da zurfafa bincike kamin daukar wani mataki.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG