Jirgin Ruwan Yakin Amurka Ya Yiwa Na Iran Harbin Gargadi

Jirgin ruwan yakin Amurka USS Nimitz

Jirgin ruwan yakin Amurka ya yi harbin gargadi ga jirgin ruwan kasar Iran ta hanyar da bai dace ba.

Iran ta fadi yau Asabar cewa wani jrigin ruwan yaki mai daukar jiragen sama, mallakin AMurka, ya yi harbi na gargadi ga wani jirgin ruwanta ta hanyar da ba ta dace ba, a cewar kafar labaran gwamnati.

Kafar labaran gwamnatin Iran ta IRNA ta ruwaito wani labari daga Rundunar Juyin Juya Hali na Iran mai cewa al'marin ya auku ne jiya Jumma'a bayan da jirgin Amurka USS Nimitz ya dumfari wata gaba mai tashar mai a tekun na Fasha sannan wani jirgi mai saukar ungulu ya taso daga jirgin na Amurka ya yi shawagi kan wani karamin jirgin ruwa mai dauke da sojojin Iran.

Wannan arangamar ita ce ta biyu a wannan satin. Ranar Talata, wani jirgin ruwan Amurka ya yi harbe-harben gargadi kan wani karamin jirgin ruwan Iran a tekun na Fasha, bayan da mutanen cikin jirgin su ka ce karamin jirgin na Iran ya tinkare su da barazana.

Iran ta karyata zargin cewa ta dunfari jirgin ruwan Amurka ranar Talata, ta ce jirgin ruwan Amurka ne ya yi ta wasu abubuwa na barazana.