Wata babban kotu a birnin Oshogbo a jihar Osun ta yanke wa wani matashi dan shekaru 40 da haihuwa Kayode Adedeji hukuncin ratayewa sabo da samun sa da laifin fashin naira 3,420 daga wata mata.
Lauya Barister Yusuf Isah Funtua yace wannan ba wani abin mamaki bane.
‘’Wannan hukuncin ba abin mamaki bane, idan aka yi la’akari da dokar Najeriya, kasan abinda doka ta tanada daban abinda kuma ido ke kallo daban. Yanzu haka doka ta Najeriya musammam dokokin da ake anfani dasu a kudancin Najeriya duk abinda ya shafi fashi hukuncin sa kenan, hukuncin ba yana laakari bane da girman abinda aka yi fashi akan sa a’a, shi fashi da makamin ne shike da wannan hukuncin, don haka baa bin mamaki bane don kotu ta samu mutun da laifin fashi da makami kuma tayi masa hukunci da kisa wannan baa bin mamaki bane.’’
To amma kuma akwai mutanen da suka sace miliyoyi wau ma biliyoyi amma ba a yanke musu hukuncin kissa ko rataya ba.
Ga Hassan Umaru Tambuwal da Karin bayani 3’22
Facebook Forum