A Pakistan, kotun kolin kasar ta haramtawa PM kasar Nawa Sharif rike ko wani mukami, kuma ta bada umarnin yayi murabus nan take.
Kakaki a ofishin PM ya bada sanarwa jim kadan bayan da kotun ta bayyana hukuncinta cewa, PM Sharif ya amince da hukuncin kotun, duk da cewa "yana da matukar shakku ko ja" da matakin, duk da haka yayi murabus.
Hukuncin yayi la'akari da cewa "saboda ya gaza ya bayyana kadarori da ya mallaka a ketare, a takardun neman takara a shekara ta 2013, kuma ya sake gabatar bayanan kadarorinsa na kariya bisa rantsuwa, hakan ya nuna cewa PM Shariff bashi da gaskiya, saboda haka an haramta masa ci gaba da zama wakili a majalisar dokoki.
Hukuncin na kotun ya ci gaba da cewa, "shugaban kasa na jamhuriyar Islam ta pakistan ya dauki dukkan matakai d a suka wajaba karkashin tsarin mulki wajen ganin cewa tsarin gwamnati na demokuradiyya ya dore."
Facebook Forum