Mai Magana da yawun sojoji masu gadin bakin teku yace an samu nasarar ceto mutane 23 daga cikin mutanen, bayan da jirgin da sukeciki ya aike da sakon neman taimakon gaggawa.
Ayoub Gassim mai Magana da yawun sojojin dake aiki a gabar teku, yace ko lokacin da suka isa wannan wuri, jirgin dake cike da ‘yan gudun hijira daga Africa ya riga ya rushe.
Yace kadan daga cikin wadanda suka rayu, yawancin su maza ne, an same su ne suna saman ruwan sakamon wani abu da suka samu suka rike, amma duk sauran sun mutu.
Libya dai nan ne wurin da bakin haure kebi domin zuwa Turai daga kasashen Africa.
Su kuma masu aikin fito nan ne suke kwasan dubban matafiyan cikin rubabbun jirage domin gitta tekun Bahar-Rum.
Wannan dai da ya faru jiya alhamis, ba shine na farko ba.