Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Tuhumar Madugun 'Yan Adawar Kasar Zambiya Da Laifin Zagon Kasa


A ranar litinin din da ta gabata ne aka kama Hakainde Hichilema saboda ya toshe hanyar da shugaban kasar Zambiya da jerin gwanonsa za su bi.

Ana tuhumar madugun ‘yan adawar kasar zambiya da laifin cin amanar kasa bayan da aka zarge shi da hana tawagar motocin shugaban kasar wucewa kwanan nan, a cewar rundunar ‘yan sandan kasar.

Shi dai Hakainde Hichilema, wanda ya ce bai amince da tsohon abokin adawarsa Edgar Lungu a matsayin shugaban kasa ba, da maraicen ranar litinin ne aka kama shi.

A lokacin da yake magana da manema labarai a birnin Lusaka, Babban jami’in ‘yan sanda, Kakoma Kakanja, ya tabattarda cewa lalle za’a tuhumi Hachilema da laifin zagon kasa.

A Zambia dai ba’a bada beli ga wadanda ake zargi da irin wannan laifin kuma laifi ne da za’a iya yanke wa mutum hukuncin kisa idan ya tabatta a kansa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG