Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Kama Babban Jagoran 'Yan Adawar Zambia


A karo na biyu cikin watanni 6 an kama babban jagoran 'yan adawa a kasar Zambia mai yawan magana kuma gabansa gadi, a cewar mai magana da yawun jam'iyyarsu a bayaninsa ga Muryar Amurka jiya Talata.

Wannan kamu wani bangare ne na takaddamar da ta biyo bayan zaben Shugaban kasa da aka gudanar a watan Agusta, wanda 'yan takarar biyu kowanne ke ikirarin shi ya ci.

Mai magana da yawun 'yan adawa Charles Kakoma ya ce 'yan sanda sun balle kofar gidan jagoran 'yan adawa Hakainde Hichilema da daren ranar Litini, su ka toshe duk wata kofar tserewa, sannan su ka jefa ma mutanen ciki barkonon tsohuwa, kana su ka yi awon gaba da Hichilema.

Kakoma ya ce zuwa har safiya 'yansanda ba su tuhumi Hichilema ba kuma sun kai shi kwalejin 'yansanda don yin masa tambayoyi. Ya ce dama an gargadi jam'iyyarsu cewa hakan na iya faruwa saboda wani al'amari cikin 'yan kwanakin da su ka gabata, inda tawagar Hichilema ta gamu da ta Shugaba Edgar Lungu yayin da mutanen biyu ke kan hanyarsu ta halarta wani taro a yammacin Zambia.

Wannan ne karo na biyu da aka kama Lungu tun daga watan Oktoban bara, lokacin da 'yansanda su ka kama shi su ka tuhumi shi da mataimakinsa da yin zagon kasa ma kasa saboda zargin da su ka yi cewa ba a yi gaskiya ba a zaben shugaban kasa na watan Agusta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG