Jirgin Masar: Al Sisi Ya Kalubalanci Kafafen Yada Labarai

Jirgin Masar Na Kamfanin Egypt Air Da Ya Yi Hadari

Shugaban Masar, Abdul Fattah al Sisi, ya gargadi kafafen yada labarai da su guji yin shaci-fadi, kan abin da ya haddasa hadarin jirgin saman Egypt Air mai lamba 804, yana mai cewa ana kan duba kowane fannin abin da ka iya haifar da hadarin.

A lokacin jawabinsa na farko da ya gabatar tun bayan faduwar jirgin, Al sisi, ya ce lallai komai zai iya faruwa, to amma “ina rokonku da ku sani cewa, yana da muhimmanci mu daina ware wani batu guda mu ce lallai shi ne ya haddasa hadarin.”

Shugaban na Masar ya kara da cewa, samun sakamakon binciken zai iya daukan lokaci mai tsawo, amma ya ba da tabbacin cewa da zarar an kammala binciken, za a sanar da mutane.

Shi dai jirgin na Egypt Air, ya fada a cikin tekun bahrurrumm ne yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa birnin Alkahira daga Paris, inda ya halaka fasinjoji da matuka