Jirgin Dakon Mai Da Aka Tsare A Equatorial Guinea Zai Koma Najeriya - Jami'ai

Wani babban jirgin ruwan na jigilar mai

Wani babban jirgin ruwa na jigilar mai da hukumomin Najeriya ke zarginsa da yunkurin lodin danyen mai ba bisa ka'ida ba, na kan hanyarsa ta komawa kasar, kamar yadda kakakin rundunar sojin ruwan Najeriya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Juma'a.

A bisa bukatar hukumomin Najeriya, kasar Equatorial Guinea ta tsare jirgin Heroic Idun, mai dauke da ganga miliyan 2 a ranar 17 ga watan Agusta, bisa laifin tafiya ba tare da wata tuta ba, yayin da ya tsere daga hannun sojojin ruwan Najeriya tare da tafiya a cikin ruwan Equatorial Guinea ba tare da izini ba.

Kakakin rundunar sojin ruwan Najeriya Commodore Kayode Ayo-Vaughan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, wasu jiragen ruwa biyu na sojojin ruwan Najeriya sun fara yiwa jirgin rakiya zuwa Najeriya da yammacin ranar Juma'a.

Binciken jirgin ruwa na Refinitiv a ranar Juma'a ya nuna cewa jirgin na kan hanya ne zuwa tsibirin Bonny da ke Najeriya.

Mai magana da yawun gwamnatin Equatorial Guinea bai amsa ba nan take don neman jin ta bakinsa. A ranar 7 ga watan Nuwamba, Teodoro Nguema Obiang Mangue, mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea kuma shugaban tsaro, ya bayyana a shafin Twitter cewa ya ba da izinin komawar jirgin zuwa Najeriya.

Najeriya dai ta ce jirgin bai yi lodin wani mai ba kafin rundunar sojin ruwa ta tunkare shi, amma ta ce jirgin ya yi karya cewa 'yan fashin teku ne suka kai masa hari, inda ya shiga wani yanki da aka takaita ba tare da izini ba sannan ya yi yunkurin lodin danyen mai ba bisa ka'ida ba.

Manajan jiragen ruwa OSM Maritime ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, a lokacin da sojojin ruwa suka tunkare shi, sun dade suna jiran takardun izini, cewa ma'aikatan jirgin sun yi imanin cewa sun fuskanci harin 'yan fashin teku ne.

Ya ce sun biya tarar Equatorial Guinea a watan Satumba, bisa alkawarin cewa za su saki jirgin da ma'aikatansa, amma kuma ci gaba da tsaren su "abin ban mamaki ne da na rashin adalci."

Hukumar Najeriyar ta ce dole ne jirgin ya koma don amsa tuhume-tuhumen da ake yi masa ko kuwa ya wanke sunansa.

Ta kara da cewa “Hakika wannan zai aike da sako mai karfi ga duk wani masu hadin gwiwa da ke da hannu wajen satar danyen mai a Najeriya, da ma kasashen duniya baki daya,”

Ma’aikatan jirgin su 26 a ranar 8 ga watan Nuwamba sun shigar da kara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja suna neman ta da ta dakatar da yunkurin mayar da su Najeriya ba bisa ka’ida ba, suna masu cewa Najeriya da Equatorial Guinea ba su da wata yarjejeniyar mika su ga kasashen waje.

Har yanzu dai ba a sanya ranar da za a yanke hukunci kan karar ba.

~ REUTERS