Jirgin kasar Japan mai zuwa duniyar sama ya isa sararrin samaniya a jiya Laraba, wanda ya kwashe kwanaki uku da rabi yana zabga gudu a kan hanyar sa ta zuwa duniyar rana. ‘Yan sama janntin sun tafi don kwaso wasu sinadarai da za’a kawo wannan duniyar don gudanar da wasu gwaje-gwaje.
Hukumar binciken sararin samaniya ta Japan ta bayyana isar jirgin wanda ya bada tazarar kimanin kilomita zuwa yankin da za’a gudanar da aikin, wanda kuma yake da nisan kimanin kilomita milliyan 280 da wannan duniyar.
Ana sa ran idan wannan aikin ya samu nasarar kaiwa da komowa na dauko sinadaran a cikin shekara daya, to babu shakka za’a samu tabbataccen bayani da zai bayyana yadda asalin hasken rana da kuma yadda rayuwa take gudana a cikin duniyar.
Wannan binciken nada matukar hadari, don haka mutunmutumin da aka aika don dauko wadannan sinadaran zasu kwashe tsawon lokaci suna neman wajen zama, da kwakulo bayanan da suka kamata, saboda tsabar zafi a duniyar na’urorin ba zasu iya aiki na miti daya ba a lokaci, sai sun rika boyewa duk cikin kowace dakika.