Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Gwajin Jirgin Sama Na Farko Mai Amfani Da Hasken Rana


Kasar Norway a karon farko tayi gwajin jirgin sama mai amfani da batiri wanda ke daukar mutane biyu kacal. Ana sa ran jirgin ya fara tashi sama a shekarar 2025, idan kungiyar jirgen sama ta bada lasisin tashin nasa.

Ministan harkokin jiragen sama na kasar Ketil Solvik, ya bayyana haka a lokacin da yake wata ganawa ta musamman, inda ya bayyana jirgin na “G2 Plane” ya kara da cewar wannan shine alamu dake muna cewar ana kara samun cigaba.

Hakan zai taimaka matuka wajen kawo karshen matsalar gurbatar yanayi da ake samu a duniya, wanda sabon jirgin mai amfani da hasken rana zai kawo karshen matsalar gurbata yanayi da man jirgi ke haddasarwa a duniya. Haka dole a tabbatar da cewar akwai duk matakan kariya wadanda mutane zasu samu natsuwa kafin su hau jirgin.

Ya kara da cewar kamfanoni kamar su Boeing da Airbus, masu kera jiragen sama sun kirkiri wasu batura masu tsada, jirgin zai rika tashi da zai kai nisan kilomita 570, ana kuma sa ran nan da shekarar 2040 duk jiragen sama na duniya zasu koma masu amfani da hasken rana.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG