Rundunar sojin saman Najeriya ta ce jirgi mara matuki ne ya fadi a Kaduna, ba jirgi mai saukar ungulu ba kamar yadda wasu rahotanni suka nuna.
Rundunar ta bayyana hakan ne bayan rahotanni da suka ruwaito cewa jirgin sojin saman kasar mai saukar ungulu ya fadi a yankin karamar hukumar Igabi da safiyar Litinin.
Sai dai a sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, rundunar ta ce ba jirgi mai saukar ungulu ba ne ya fadi, tana mai cewa wani jirgi mara matuki ne ya samu matsala bayan da ya tashi.
“Duba da cewa jirgi ne mara matuki, ba a samu wani da ya mutu ko ya ji rauni ba.” In ji wata sanarwa da darektan yada labarai, Air Vice marshal Edward Gabkwet ya wallafa a shafin Facebook na rundunar.
Ya kara da cewa, tuni an kaddamar da bincike domin gano abin da ya haddasa hatsarin.
“Muna masu tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa wannan ‘yar tangarda da aka samu, ba za ta kawo cikas akan ayyukanmu ba.”