Kungiyar agaji da ake kira Syrian Civil Defense da turanci, tace jiragen yakin kasar masu saukar ungulu ne suka kai hari da mamakai masu guba da ake kira Chlorine a wata unguwa da ake kira al-Sukkari dake hanun 'yan tawaye.
Zargin amfani da makamai masu guba ba sabon abu bane a rikicin da ake yi a Syria, inda duka sasssan biyu suke zaergin juna da amfani da makaman.
Ahalinda ake ciki kuma, Turkiyya tace a shirye take ta shiga duk wani matakin soji dda Amurka zata dauka nan gaba da zummar 'yanto birnin Raqqa daka hanun ISIS, kamar yadda shugaban kasar Rajib Tayyip Erdogan ya fada.
Kafofin yada labarai na kasar sun ce Erdogan ya fadawa ayarin 'yan jarida wadanda suke balaguro da shi kan hanyar komawarsu gida daga taron koli na kasashe da suke kungiyar da ake kira G20, cewa sun yi magana kan haka a gefen taron kolin da aka yi a China, a zaman da suka yi da shugaban Amurka Barack Obama.
Shugaba Erdogan yace, ana sa ran jami'an sojojin kasashen biyu zasu gana domin su tattauna batun 'yanto birnin na Raqqa daga hanun ISIS.