Harin da aka kai kan tashar bincike ta kauyen Tamou a ranar Asabar 22 ga watan Oktoba da wanda aka kai a tasha ta biyu ta wannan gari a ranar Litinin 24 ga watan na Oktoba wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan sanda biyu tare da kwashe bindigogi da harsasai, sun sa hukumomin tsaro tura jiragen sama masu saukar ungulu guda biyu farautar maharan wadanda bayan shawagi na dan takadirin lokaci aka hango su suna kokarin buya a karkashin rumfa gab da wata mahakar zinare ta bayan fage da ke gabashin kauyen Tamou a gundumar Say a jihar Tilabery, a cewar wata sanarwar da ma’aikatar tsaron Nijer ta fidda.
Barin wutar da wadannan jirage suka yi a wurin da abin ya faru yayi sanadiyyar hallaka mutane biyar tare da lalata makaman da suka sata. Shugaban kungiyar kare hakkin jama’a ta Voix des sans Voix Alhaji Nassirou Saidou, wanda ya yaba da abinda ya kira jajircewar askarawan Nijer, ya yi kira ga hukumomi da su kara jan damara don kakkabe ‘yan ta’adda daga sassan kasar.
Sanarwar ta kara da cewa a lokacin da hukumomi suka ziyarci asibitin garin likitoci sun sanar da mutuwar mutane bakwai yayin da aka kwantar da mutane ashirin da hudu da suka ji rauni a asibitin Say da wasu asibitocin birnin Yamai, sai dai wasu ‘yan fafutika na ganin bukatar gudanar da bincike domin gano zahirin gaskiyar lamari kasancewar bayanai na cin karo da juna a game da harin, inji Maikoul Zodi shugaban kungiyar Tournons La Page Internationale.
A karshen watan Satumban da ya gabata ne hukumomin gundumar Say suka rufe mahakar zinaren garin Tamou da ke wani sashe na kebebben gandun dajin Parc National du W da ke kan iyakar Nijer da Burkina Faso, a cewarsu matakin na matsayin wani bangare na kokarin kare al’ummar yankin daga barazanar tsaron da ake fuskanta.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5