Jiragen Sojin Najeriya sun Dakile Harin Boko Haram A Jihar Yobe

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta sami nasarar dakile wani harin 'yan kungiyar Boko Haram, ta hanyar amfani da jiragen yaki, inda suka fatattaki mayakan a garin Geidam da ke jihar Yobe.

Majiyoyi daga jihar Yobe dai sun yi nuni da cewa, mayakan na Boko Haram, sun mamaye garin Geidam da manyan motocin yaki kimanin 10, don afka wa mutane yayin da suke shirin shan ruwa da yammacin jiya Juma’a

To amma rundunonin tsaron Najeriya da suka hada da sojojin kasa da na sama sun fatattaki maharan, lamarin da ya yi sanadiyar hallaka kimanin maharan 10 sakamakon ruwan bama-bamai da jiragen soji suka yi musu.

Garin Geidam ne mahaifar tsohon gwmanan jihar ta Yobe, Ibrahim Geidam, da kuma sabon babban sufeton 'yan sandan Najeriya Usman Baba Alkali wanda ya dare kan kujerar a kwanan nan.

Usman Alkali, Mukaddashin Sufeto Janar Na 'yan Sandan Najeriya

Kamar yadda wata majiya ta bayyana wa jaridar PRNigeria, duk da cewa sojojin kasa sun fatattaki wasu 'yan ta'adda da suka gudu bayan dakile harin, babu tabbacin ainihin adadin wadanda aka kashe daga cikinsu.

Karin bayani akan: ‘yan bindiga​, Boko Haram, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

ASP Dungus Abdulkarim, wanda ke zama mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Yobe, ya fadawa manema labarai cewa, mayakan na Boko Haram sun rika watsawa mutane wasu takardu dake kunshe da sakon cewa sun zo ne da zummar kafa daular Islama.

Takardar da Boko Haram Suka Rarraba A Geidam

Idan ana iya tunawa, makamacin wannan harin ya auku a ranar 13 ga watan Afrilu, lokacin da sojojin Najeriya suka dakile hare-haren ta'addanci da yawa da aka yi niyyar kai wa sojoji da wasu Musulmai a lokacin buda bakin Azumin Ramadana, a garin Damasak da ke Jihar Borno.

Haka kuma, majiyoyin sun ce sojojin kasa na sun samu dauki daga jiragen saman rundunar sojin saman kasar dake garurruwan Damasak da Gajiram bayan da 'yan kungiyar ta Najeriya suka far musu.

Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

Wata majiyar leken asirin soji ta fada wa PRNigeria cewa 'yan ta'addar na kan hanyarsu ta daukar fansar fitattun kwamandojinsu 13 da sojoji suka kashe a yankin Tafkin Chadi a kwanakin baya.

An dai kwashe sama da shekaru goma ana fuskantar rikicin mayakan Boko Haram dake ikirarin kafa daular Islama a yankunan arewa maso gabas.

Shi kuwa yankin arewa maso yamma yana fama ne da hare-haren ‘yan bindiga dadi masu satar mutane domin karbar kudin fansa, inda kusan duk lokacin da miyagun suka kai hari, gwamnatin Najeriya ke cewa tana kokarin kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.