Wasu masana ilimin tsirrai da tsuntsaye na wani aikin agaji ga tsuntsayen Aku da bala’in guguwar Hurricane Maria, ta abkawa kasar Puerto Rico a yankin kudancin Amurka a watannin baya.
Nau’in tsuntsayen Aku masu ruwan tsanwa basu da yawa a fadin duniya, kuma sune jinsin da sukafi kaifin basira a baki dayan halitar Akukkuturu a doron kasa.
Tun bayan barnar guguwar ta Maria a cikin kungurmin dajin El Yunque a kasar, kimanin jinsin tsuntsaye biyu ne cikin 56 dake rayuwa cikin dajin suka rayu, bayan guguwar mai karfin muraba’in ma’auni na 4 da aka samu a watan Satumbar shekarar 2017.
Akalla kimanin 4 cikin 31 na nau’ukan tsuntsaye a dajin suka rayu, a wani kauyen kudancin Maricao, tare da Aku 75 cikin 134 da suke rayuwa a yankin suka rage a cewar manazartan, hakan yasa suke aikin ceton ran wadanda suka rage.
Rashin tsiradda rayukan Akukuturun na iyasa a rasa irin wannan nau’ukkan na Akun a fadin duniya.