A shirinmu na matasa da siyasa a wannan mako, mun sami bakuncin Haruna Kabiru, wanda aka fi sani da Haruna wakili, matashin dan siyasa wanda ya ce an bai wa matasa da ma da kudurin nan na 'not too young to run’ babban abin alheri ne kan makomar siyasar matasan Najeriya.
Haruna Wakili ya ce lokaci ya yi da za’a daina wasa da kwakwawar matasa da kudi ko wani abin duniya tsabanin haka za su yi amfani da shafukan sadarwa domin tallata dan takararsu cikin sauki da tsafta tare da yada manufofin cigaban kasa.
A yanzu babban abin da ake bukata ga su matasa shi ne su tallafawa 'yan uwansu matasa domin cimma wannan matsaya cikin sauki ta hanyar dakile wannan dabi’ar na karbar kudi ko siyasar kasuwar bukata.
A wannan zabe matasa na sa ran za su kada wasu 'yan siyasun da suka ga jiya suke kuma ganin yau domin a sakar wa matasa mara, wannan sauyi kuma shi ne zai kawo karshen 'yan siyasa manya a Najeriya .
Facebook Forum