Gwamnatin jihar Plateau tace zata farfado da dokar biyan haraji gadan gadan don samin kudaden shiga da zai bata sukunin aiwatar wa Jama’a ayyukan more rayuwa.
WASHINGTON, DC —
Kwamishinan yada labaran jihar Plateau Mallam Mohammad Nazif, a wani taron manema labarai ya bayyyana cewa zamani ya wuce da jihar zata ci gaba da dogaro da gwamnatin Tarayya, musammam ma a wannan lokaci da tattalin arziki ke tangal tangal.
Jihar dai ta tsara wasu abubuwa guda Uku da za a sami kudin shiga, na farko harajin kasa da fannin Gona sai kuma na Uku shine guraren yawan shakatawa.
A ra’ayin wasu mutanen jihar na cewa yana da matukar amfani ayi hakan domin yawancin kasashen da suka ci gaba a Duniya, suna karba kuma suna taimakawa al’umma ta hanyar gina kasa. Sai dai kuma a cewar wasu mutanen jihar na ganin hakan zai musgunawa mutane domin babu wasu hanyoyin samun kudi.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5