Uwar Jam’iyyar ta kasa baki daya tace matakin jam’iyyar a jihar Yobe, ba dai dai bane kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Babban lauya Dakta Muiz Banire, wanda yake shine mashawarcin jam’iyyar APC ta kasa baki daya kan harkokin Shari’a, yace “idan ka duba kundin tsarin mulkin Jam’iyyar mu babu wani reshen jam’iyyar da ya isa ya kori ‘ya ‘yan jam’iyya, sai majalisar zartarwa ta kasa baki daya..” ya ci gaba da cewa idan akwai wani mataki ba wanda ya fada to shiriri ta ne.
Sai dai kuma jam’iyyar APC a jihar Yobe, tace bata gamsu da matsayin uwar jam’iyyar ta kasa ba, a cewar shugaban jam’iyyar na jihar Alhaji Adamu Chillare, yace mai baiwa jam’iyya shawara kan harkokin Shari’a bai isa yace ya mayar da hukuncin da suka yanke a jiha. Alhaji Adamu yace idan har wasika bata fito daga ofishin shugaban Jam’iyya na kasa ba to bazasu canja hukuncin su ba.
Domin karin bayani.