Kungiyar dai tace karin kudin Buredin ya zame mata tilas bisa la’akari da asarar da suke tafkawa tun bayan da farashin kayan masarufi ya tashi a Najeriya.
Tuni dai masu amfani da Buredi na yau da kullum musammam talakawa ke kokawa akan karin farashin Buredin. Alhaji Lawali Shukura, shine ma’ajin kungiyar masu gasa Buredi a jihar Neja, yayi karin haske akan sabon farashin inda yace dole ce ta sasu kara kudin, ya kuma yi kira ga sauran al’umma da suyi hakuri ga halin da baki daya kowa ya tsinci kansa.
Buredin da duk ake saya akan Naira 120 yanzu ya koma Naira N140, wanda ake saye akan N200 yanzu za a iya samun sa akan N250, na N250 kuma ya koma N300, wanda a baya ake saya N50 yanzu ya koma N60.
Duk da cewa ana kara samun hauhawar farashin kayan abinci a cikin wannan lokaci, gwamnatin kasar tace tana iya kokarin ta wajen shawo kan al’amarin, tare da kokarin samar da aikin yi a tsakanin yan kasar.
Domin karin bayani.