Hakan ne ya sa gwamnan Jihar, Abubakar Sani Bello, ya ba da umurnin a dauki karin ma’aikatan kiwon lafiya a jihar.
Wannan mataki ya biyo bayan wata ziyarar ba za ta da gwamnan ya kai ne a asibiti inda ya tarar babu likitocin da za su saurari dumbin marasa lafiya da suka yi dafifi.
“Na je asibiti misalin karfe uku har zuwa karfe goman dare babu likita ba, a lokacin na kira sakataren na dindindin a ma’aikatar kiwon lafiya na gaya mai cewa a dauki likitoci a aiki.” In ji Gwamna Bello.
Sai dai masu sa ido kan al’amuran yau da kullum sun ce duk da cewa gwamnan ya yi abin a yaba da ya ba da wannan umurni, kamata ya yi a ce an gudanar da bincike domin a gane wadanne ma’aikatan kiwon lafiya ne ba su je aiki ba a daren.
Baya ga batun matsalar da ke tattare a fannin kiwon lafiyar kasar, akwai rashin abun hanu da ‘yan jihar ke korafin babu, wanda hakan ke sa mutane da dama su fi dogaro a kan asibitocin gwamnati da suka fi sauki
Saurari wannan rahoton Mustapha Nasiru Batsari domin jin yadda al’umar jihar ke kokawa da rashin kudi a hanu:
Your browser doesn’t support HTML5