Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Yaba da Cire Najeriya daga Jerin Kasashe Masu Cutar Polio


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta Wanke Najeriya daga Cutar Shan Inna ko Polio

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana farin cikinsa da cire Najeriya daga jerin kasashen da suke fama da cutar shan inna ko Polio saboda fiye da shekara daya b'a samu bullar cutar ba a koina a fadin kasar.

Yau watanni 14 ke nan da ba'a samu wanda ya kamu da kwayar cutar ba. Shugaba Buhari yace an shaida masa cewa rashin kamuwa da kwayar cutar a koina a kasar shi ne matakin farko da hukumar kiwon lafiya ta duniya zata bata takardar shaidata ta din-din-din nan da shekaru biyu masu zuwa.

Shugaba Buhari yace ya tuna shugabar hukumar Dr Margaret Chan ta ambaci wannan nasarar da Najeriya ta samu a taron Majalisar Dinkin Duniya na saba'in da aka yi watan jiya a birnin New York. Saboda haka ya yabawa hukumar da hakikancewarta na tabbatar da lafiyar duniya gaba daya.

Shugaba Buhari yace kamar yadda aka sani Najeriya ta soma fafutika da cutar ne gadan gadan tun shekarar 1998. Yace cutar ta yi muguwar illa ga "kasarmu" dangane da nakasa da ta yiwa mutane tare da kadarorin da kasar ta yi anfani dasu. Yace duk da nasarar "ba zamu yi lago a kafa ba domin mun dukufa mu cimma muradunmu da kuma kiyaye rayuwar 'ya'yanmu daga nakasar cutar polio"

Shugaba Buhari ya cigaba da cewa ba zasu yi sako-sako ba amma "zamu inganta yadda muke kiyayewa da kula da 'ya'yanmu da allurai rigakafi domin cigaba da dakile cutar. Yace gwamnatin tarayya zata cigaba da yin sheilar gaggawa akan cutar daga yanzu har shekaru biyu masu zuwa.

XS
SM
MD
LG