Za a fara wasan ne da taka leda a shahararren filin wasa na Azteca dake babban birnin Mexico a ranar 11 ga watan Yuni.
A biranen Atlanta da Dallas zasu karbi bakuncin wasannin kusa da karshe, yayin da za a buga wasa a mataki na 3 a birnin Miami.
Sai wasannin quarter-final da za a buga a biranen Los Angeles, Kansas, Miami da Boston.
Jimlar birane 16 a fadin kasashen 3 za su dauki bakuncin wasannin, yayin da mafi yawa daga cikin wasannin za a yi su ne a cikin Amurka.
A baya an buga gasar cin kofin duniya na shekarar 1994 a Amurka inda aka yi wasan karshe a Rose Bowl da ke Pasadena, a kusa da Los Angeles.
An sanar da matakin ne ta wani shirin talabijin da aka watsa a Amurka ta arewa wanda ya nuna shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino tare da dan wasan barkwancin nan kuma dan wasan fina-finan hollywood Kevin Hart, da mawaki Drake, da kuma Kim Kardashian.