Kuma tuni hukumomin kasar suka isa wurin don neman kungiyar da ta gaggauta kamalla aikin da zai samarwa matasa aikin yi, da ba da damar girka masana'antu da dama, wannan ko biyo bayan daukar darasi da kasar ta ce ta yi bayan datse mata wuta da Najeriyav ta yi sanadiyyar juyin mulki a 2023
Biyo bayan hambare Bazum Mohamed daga kan karagar mulki ne, kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Africa ECOWAS/CEDEAO ta karkabawa Nijar takunkumai ciki ko har da cirewa kasar wutar lantarki daga Tarrayar Najeriya.
Kuma tun a wannan lokacin ne, 'yan kasar da hukumomin mulkin sojan kasar suka soma tunanin hanyoyin kaucewa sake fadawa wannan matsalar, abin da ya sa, wadansu 'yan kasar ta Nijar da wata kungiyar kasar Birtaniya mai suna Savannah Energie, suka soma aikin dasa turukan na'urori masu anfani da kadawar iska da zai baiwa kasar Megawatts 250 a garin Magaria Makera tsakanin gundumomin Malbaza da Madawa a cikin jihar Tahoua.
In za a tuna, ministan makamashin kasar Farfesa Amadu Haoua da rakiyar gwamnan jihar Tahoua suka garzaya a wurin don neman ganin kampanin ya gaugauta wannan aikin, tare da kamallawa a cikin lokaci.
Wannan aikin zai baiwa kasar damar samun kaifin wutar lantarkin da zai kai kashi 22 cikin 100 na bukatar kasar, yayin da za'a anfani da turuka 45 da zai ba da Jigawatts kusan 800 a kowace shekara.
Saurari cikakken rahoto daga:Harouna Mamane Bako:
Your browser doesn’t support HTML5