JIHAR KWARA: An Kashe Fulani Tare da Kone Gawarwakinsu a Yankin Pategi

Fulani makiyaya.

A wani hari da Fulani suka ce an kai masu a yankin Pategi kimanin su ashirin aka kashe tare da kone gawarwakinsu da gidajensu

Kimanin Fulani makiyaya ashirin aka kashe tare da kona gawarwakinsu a yankin Pategi dake jihar Kwaran Najeriya sanadiyar wani hari da aka kai masu.

Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah reshen Kwara Alhaji Usman Adamu ya shaidawa Muryar Amurka cewa harta gidajensu da wasu kaddarorinsu an kona sakamakon harin. Yace an dauki mako guda ana kai masu hari jefi-jefi. Yace har yanzu lamarin bai tsaya ba. Yace an kashe yara da mata da tsoffi ba tare da wani dalili ba.

An kashe yara Fulani tara a wani kauyen Gureke, kana an sake kashe wasu guda takwas da aka kone gawarwakinsu. An kone masu ababen hawa, abincinsu da dabbobi.

Kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya tace ta samu labarin tashin hankalin kuma tana daukan mataki kamar yadda mataimakin shugaban kungiyar na kasa Alhaji Useini Boso ya sanar. Yace zasu rubutawa gwamnan jihar da sarkin Pategi. Yace yana ganin ba daidai ba ne a kebe wata kabila a ce za'a kawar da ita daga doron kasar duniya.

Bayanai daga yankin sun ce rikici aka samu tsakanin Nufawa da Fulani dake yankin. Amma sakataren masarautar Pategi Alhaji Muhammad Ibrahim yace lamari ne na shaidan kuma kawo yanzu an shawo kan matsalar. Yace kwamishanan 'yan sanda Alhaji Salihu Garba ya aiko an zauna an daidaita da juna.Yace an kira bangarorin biyu an tattauna. Yanzu babu komi.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

JIHAR KWARA: An Kashe Fulani Tare da Kone Gawarwakinsu a Yankin Pategi -2' 47"