Da ya ke gabatar da rahoton tsaro na watanni ukun farkon wannan shekara a gaban kwamitin tsaro na jahar Kaduna, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar, Malam Samuel Aruwan ya ce adadin mutanen da aka kashe a watannin sun haura wadanda aka kashe a irin wadannan watanni a bara.
Bisa ga cewar kwamishinan, a cikin watanni ukun na farko an kashe mutane dari uku da sittin suka kuma yi garkuwa da 1389 a cikin watanni uku na farkon wannan shekarar, yayinda su ka ji wa mutane 258, aka kuma yi wa mata 10 fyade yayin kai hare haren, aka kuma sace dabbobi 3251. Lamarin da ya ce ya ta'azzara.
Bayyana ta'azzarar matsalar tsaron a jahar Kaduna daga bakin gwamnati, ya sa masana harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai ritaya nuna damuwa.
A hirar shi da Muryar Amurka, Majo Shinko ya bayyana cewa, ganin gwamnati ta fita karara ta ce lamarin ya ta'azzara manuniya ce cewa, lamarin yana nema ya fi karfin gwamnati. Bisa ga cewarshi, fitowa kullum da gwamnatin tarayya ta ke yi tana cewa, tana iyaka kokarinta ba wani abu ne da ke da tasiri ga al'umma ba, kasancewa lamarin sai karuwa ya ke yi kullum.
Sai dai kuma duk da matsalolin tsaron da aka samu cikin watanni ukun farkon wannan shekara, kwamishinan tsaro Malam Samuel Aruwan ya ce akwai wasu nasarori da aka samu.
Rahoton watanni ukun farkon wannan shekara dai ya nuna adadin mutanen da 'yan-bindiga su ka kashe ya haura na bara da mutane 46 yayin da adadin wadanda aka yi garkuwa da su suka haura da mutane 440.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5