A yayinda Muryar Amurka ta zanta da kwamishana ilimin jihar Borno, Inuwa Musa Kubo akan jita-jitaR dake yawo cikin jihar cewa an rufe makarntun mata, ya bayyana abun da gwamnati ta yi maimakon rufe makarantun.
A cewarsa makarantunsu na aiki amma da aka debe 'yan matam Chibok sai gwamnati ta sake shawara .Dalili ke nan da gwamnati ta kaurar da duk makarantun 'yan mata na kwana zuwa Maiduguri da Biu inda ake da tsaro sosai. Amma cewa an rufe makarantun jihar Borno ba gaskiya ba ne a cewar kwamishanan.
Inuwa Kubo ya ci gaba da cewa manufarsu ita ce su tabbatar babu wata makarantar 'yan mata a wurin da bashi da ingantacen tsaro. Da zara an samu ingantacen tsaro a wasu wuraren za'a mayar da makarantun.
Baicin makarantun 'yan mata akwai wasu makarantun dake wuraren da babu ingantacen tsaro su ma an kwashesu an kaisu inda akwai tsaro. Ya bada misalan makarantun da ba na mata ba da aka kaurar da dasu zuwa wurae daban daban.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5