Kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu inji ta bakin shugabanta na jihohin Adamawa da Taraba Alhaji Dahiru Buba ta danganta tashin farashin kananzir din da fasa bututun man matatun kasa da ‘yan tsageran Naija Delta suak yi da kuma cire tallafi da gwamnatin tarayya ta yi cikin watanni goma sha biyar daga naira arba’in da kobo casa’in zuwa naira dari da talatin da biyar.
Bincike da wakilinmu Sanusi Adamu ya gudanar ya nuna ana sayar da gallon naira dubu daya da dari biyar a kasuwar bayan fage maimakon naira dari bakwai da hamsi da biyar kamar yadda gwamnati ta kayyade, wannan ya sa magidanta irinsu Peter Abdu Gabai da Patient Yohana suka koma ga anfani da itace a maimakon kanazir.
Wani mai saida man kananzir a bayan fage Ahmed Kabiru ya shaida mani cewa suna samun hajarsu a gidajen mai inda ake dora masu wani abu akan farashin da gwamnati ta kayyade dalili da ya sa suka kara wa kananzir din farashi.
Sai dai sabanin tsammanin da ake yi tashin farashin kananzir zai kawo bunkasar masu sana’ar sayar da itace, Nasiru Hamidu mai sana’ar sayar da itace a motar a-kori-kura ya ce al’amarin ba haka yake ba. Ya ce suna kawanaki baya sun yi kafa daya kamin su sake komawa daji saboda koken jama’a na matsin halin rayuwa da talakawa ke ciki.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5