Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Buhari Ta Kara Kaimi Kan Taimakon 'Yan Gudun Hijira A Arewa Maso Gabas


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Gwamnatin Najeriya da Muhammad Buhari ke jagoranta ta kara yawan taimakon abinci da na wuraren kwana da magunguna wa duk sansanin 'yan gudun hijira dake arewa maso gabashin kasar domin inganta rayuwar mutanen da suka tagayyara sanadiyar rikicin Boko Haram.

Buhunhunan hatsi fiye da dubu dari ishirin da uku da kayan wuraren kwanciya fiye da dubu biyu da dari daya da hamsin da biyar ne hukumomin gwamnatin suka samar ma wadannan bayin Allah da rikicin Boko Haram ya daidaita a arewa maso gabashin kasar.

Karin taimakon yana cikin kokarin da gwamnatin keyi domin ceto mutanen cikin gaggawa musamman wadanda yunwa ta shigesu sosai domin 'yan ta'adan da suka tsaresu wata da watanni da kyar suke basu abinci sau daya rana.

A karkashin wannan shirin na gaggawa kwamitin kula da 'yan gudun hijira na fadar shugaban kasa dake arewa maso gabas da hukumar bada agajin gaggawa ta gwamnatin tarayya su ne kan gaba wurin raba buhunhunan abinci kimanin dubu goma da dari uku.

Kayan abncin ko sun hada da shinkafa da dawa da gyero da masara, da gishiri da mai da wake da dai sauransu da aka kai jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Gombe da Bauchi.

Baicin wadannan kayan hukumar bada agajin gaggawa ta gwamnatin tarayyar ta karawa jihar Borno buhunhunan kayan abinci dubu goma sha uku da dari biyu.

Kayayyakin Abinci Domin Tallafawa 'Yan Gudun Hijira A Jihar Borno
Kayayyakin Abinci Domin Tallafawa 'Yan Gudun Hijira A Jihar Borno

Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ma ya rabawa wasu kananan hukumomi tara a jihar Borno kayan kwanciya dubu biyu da dari daya da hamsin da biyar. Kananan hukumomin ko sun hada da Bama, Damboa,Bakaci, Dikwa, Monguno, Mafa, Jere Banki da Gwoza.

Cikin gaggawa gwamnatin tarayya ta kwashe yara da mutanen da rahotanni suka ce ransu na hannun Allah saboda tsananain yunwa daga Bama zuwa Maiduguri domin su samu kulawa sosai,\.

Kazalika gwamnatin ta umurci ma'aikatar kiwon lafiya ta kasa da ta rundunar sojin mayakan sama da su kai agaji na musamman a sansanin dake Bama.

Haka ma ita gwamnatin Bornon ta mayar da wata makarantar Islamiya dake Bama ta zama asibiti. Rundunar mayakan sama zata kai kayan aikin da aka bukata a asibitin domin kula da mutanen dake bukatar jinya cikin gaggawa.

Idan ba'a manta ba tun can baya Shugaba Muhammad Buhari, a cigaba da kokarinsa na ceto yankin arewa maso gabas daga hannun 'yan ta'ada ya bada umurnin kafa wani kwamiti na musamman akan yankin. Janar Theophilus Danjuma mai murabus shi ne shugaban kwamitin da aka dorawa alhakin sake gina yankin na arewa maso gabas.

XS
SM
MD
LG