Anyiwa matar nan data jefi shugaban kasar Venezuela aka da mangoro alkawarin sabon gida, labarin daya bazama ko ina a fadin kasar.
Satin daya wuce ne shugaban kasar Nicolas Maduro ‘dan shekaru 52 da haihuwa ya tuka motar bus cikin ‘dinbin mutane a titin dake cibiyar jihar Aragua a kasar, daga cikin ‘dinbin mutanen dake gefen titi wani ko wata da ba’a san kowaye ba ya jefi shugaban da mangoro aka.
A jikin mangoron dai an rubuta “idan zaka iya, ka kirani” tare da lambar waya, alokacin da shugaban yake nuna mangoron a gidan talabishin.
Ita dai matar data jefi shugaban tana fuskantar matsala da gidan da take zaune ciki, jami’an gwamnatin kasar suka kira ta, ta amsa cikin tsoro, jami’in yace mata an amince da a baki sabon gida, cikin manufofin samar da muhalli na wannan gwamnati, kuma shugaban kasa yayi alkawarin shan mangoran da kika jefe shi da shi.
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro, na da halin jin kai ga talakawan kasar sa, haka wasu lokuta kan yi kyautar gidaje, kayayyakin amfani, kai harma da kyautar biyan fansho ga masu kananan karfi.