Jibi Laraba Za A Fara Ciro Mahaka Ma'adinai Su 33 A Kasar Chile

Ma'aikata su na cusa bututun karfe domin hana ramin da aka haka na ceto ma'aikatan rusawa a lokacin da ake kokarin zakulo su.

Ma’aikata na kasar Chile su na kara karfin wani ramin da za a yi amfani da shi wajen ceto mahaka ma’adinai su 33 wadanda suka shafe watanni biyu da kwanaki a karkashin kasa

Ma’aikata na kasar Chile su na kara karfin wani ramin da za a yi amfani da shi wajen ceto mahaka ma’adinai su 33 wadanda suka shafe watanni biyu da kwanaki a karkashin kasa.

Ma’aikata sun fara jera bututun karfe a kewayen wannan rami jiya lahadi, domin tabbatar da cewa gugar da za a yi amfani da ita wajen zakulo mutanen ba ta harde a cikin wannan ramin ba. Za a yi amfani da gugar wajen dauko mahakan, daya bayan daya, ta cikin wannan rami na musamman da aka haka.

Ministan hakar ma’adinai na Chile, Laurence Golborne, yace watakila za a fara fito da mahakan a ranar laraba, a bayan an sanya injin da zai ringa janyo gugar. Ana sa ran za a dauki kwanaki biyu ana aikin fito da mahakan daya bayan daya.

Ministan kiwon lafiya na Chile, Jaime Manalich yace mahakan dake karkashin kasa sun bayyana kwarin guiwa sosai kan yadda za a ceto su har ma sun fara gardama a tsakaninsu kan kowannensu yana son ya zamo shi ne na karshe da za a fitar. Yace ba mai son zamowa na farko-farko da za a fitar daga wuri mai zurfin mita 600 da suke.