Jerin Sunayen Sabbin Ministoci A Yanar Gizo, Gaskiya Ko Farfaganda? 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu lokacin bude taron kaddamar da majalisar tattalin arzikin kasa

An shafe daren jiya a Najeriya ana yayata jerin sunayen wadanda ake cewa, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ke shirin zaba a matsayin Ministoci, a kafofin sada zumunta na yanar gizo duk da yake babu wata majiya a hukumance da ta tabbatar da haka.

ABUJA, NIGERIA - Wannan dai ba shi ne karon farko da aka fitar da jerin sunayen "sababbin Ministocin" ba tun bayan rantsar da Bola Tinubu Shugaban kasa.

Duk da ana sa ran Shugaba Tinubu zai mika sunayen Ministocinsa ga Majalisar Dattawa nan ba da dadewa ba; amma wadanda su ka bayyana zuwa yanzu sun zama tamkar na fatan alheri ne ko yada farafaganda da wasu ke yi don tallata sunayen wasu gwanayensu.

Abun da ya fito fili a sunayen da a ka yayata da ba sunan wanda ya fitar da sanarwar kamar yadda ake gani a bayanai masu tushe daga daraktan labarai na ofishin Sakataren Gwamnati Willie Bassey ko ma kakakin Shugaba Tinubu, Dele Alake.

A hirar shi da Muryar Amurka, dan kwamitin gudanarwa na APC Dattuwa Ali Kumo ya ce ba bukatar gaggawa daga wadanda su ka yada bayanan marar sa tushe amma jerin hakika na tafe.

Za a jira a ga wadanda za su zama Ministocin Gwamnatin Tinubu da a ka ce 'yan siyasa za su ci gajiya kuma za a yi la'akari da gudunmawa daga jiha ko shawarar gwamnoni maimakon yadda tsohon shugaba Buhari ya nada Ministocin sa bisa ga wadanda ya sani ko ya gamsu ya yi aiki da su.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Jerin Sunayen Sabbin Ministoci Ya Bazu A Yanar Gizo, Gaskiya Ko Farafaganda? .mp3